Koma Labarai
Labarai

Sanata Barau ya kori hadimin sa, King Indara kan wallafa saƙon 'Abba Must Go' a shafukan sadarwa.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sanata Barau ya kori hadimin sa, King Indara kan wallafa saƙon 'Abba Must Go' a shafukan sadarwa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin Maliya, ya kori Sarkin Matasa Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara, daga muƙaminsa na Mai Taimaka Masa na Musamman (SLA) saboda wallafa "Abba Must Go" a kafafen sada zumunta.

Hakan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai, Shitu Madaki Kunchi, ya fitar a ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.

Kazalika, sanarwar ta ce, an sallami King Indara, ne daga muƙamin sakamakon rubuce-rubucen da ya yi a kafafen sada zumunta na Abba Must Go, waɗanda ofishin ya bayyana a matsayin rashin ladabi ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwar ta ce rubuce-rubucen sun saɓa da tarbiyya da mutuntakar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma tsarin APC, musamman umarninsa na girmama jam’iyyar daga sama har ƙasa.

Kafar Arewa updates ta ruwaito cewa, Sanarwar ta kuma ce sallamar King Indara daga muƙamin SLA, ta fara aiki ne daga ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.

Ready to PlayDala FM88.5 FM