Koma Labarai
Tsaro

Rundunar ƴan sandan Kano ta kama sama da motoci 80 waɗanda ake rufe lambobin su, wasu ma babu lambar.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar ƴan sandan Kano ta kama sama da motoci 80 waɗanda ake rufe lambobin su, wasu ma babu lambar.

Rundunar ƴan sanadan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama sama da motoci guda 80 waɗanda ake rufe lambarsu wasu ma ba a sanya musu lambar ba gaba ɗaya.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Kwamishinan yansandan jihar Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Litinin 6 ga Yuli, 2026.

Sanarwar ta ce, "Kasancewar babban aikin Ƴan Sanda, shi ne kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da kiyaye doka da oda, kuma a kwanan nan, rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta lura da ƙaruwar yawan motocin da ke yawo a kan titunan jihar lamba a rufe, ko kuma babu lamba kwata-kwata," in ji shi.

A cewar ƴan sandan, wannan ba ƙaramin laifin zirga-zirga ba ce, tana mai cewa yunƙuri ne da gangan na ɓoye abin laifi, kasancewar masu laifi suna amfani da irin waɗannan motocin wajen aikata laifuka sannan su gudu ba tare da an gane su ba.

Rundunar ƴan sandan ta Kano, ta kuma ce ba za ta lamunci jihar ta zama matattarar masu irin waɗannan ayyuka ba.

CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ƙara da cewa, kafin a fara aiwatar da wannan doka a ƙarƙashin jagorancin da, an gudanar da wayar da wayar da kan jama'a mai yawa, "Mun tunatar da masu motoci a kan alhakinsu na yin rajistar motoci da kuma tabbatar da an sanya lamba a bayyane, kuma mun yi sanarwa da yawa, domin babu wanda zai ce bai sani ba," in ji CP Bakori.

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma ce, zuwa wannan lokaci sun kama motoci 72, waɗanda suka saɓawa doka, kuma an ajiye su inda dorebobin za su fuskanci hukunci.

A cewar sa, "An kuma kama motoci 3, waɗanda masu motocin suka kasa ba da cikakken bayani a kan mallakar motoci da dalilin amfani da su, kuma ana ci gaba da bincike a kansu, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan su," in ji shi.

Ya ce za su ɗauki matakin ba Sani ba sabo ga duk wanda suka kama motar sa ba lamba ko kuma ya rufe ta.

CP Ibrahim Bakori ya kuma yi kira ga jama'a da su baiwa Ƴan Sanda haɗin kai, su kuma guji yin duk wani abu da zai kawo tarzoma, kuma duk wani jami'in su da ya fake da wannan aiki yana zaluntar mutane ka da a yi shiru a sanar da rundunar ta waɗannan lambobin wayar 09134558533, ko 08115657624.

Ready to PlayDala FM88.5 FM