Hisbah ta kama ƴan daudu 12 da mata masu zaman kansu 10, suna shirin raƙashewa a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta samu nasarar dakile wani bikin raƙashewa da wasu da ake zargin ƴan daudu ne da kuma mata masu zaman kan su suka shirya gudanarwa a kan titin gidanzu wato zoo road.
Mukaddashin kwamandan hukumar hisban na jihar Kano Dr. Mujahideen Amunidden Abubakar ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aiko wa Dala FM Kano.
Ya ce tuni suka kama waɗanda ake zargi da yunkurin gudanar da bikin mara kyau, inda aka samu yawancin su suna kawalci, wasu kuma na zaman kansu.
A cewar sa, hukumar ta kama maza guda 12, mata kuma guda 10, kuma za su fadaɗa bincike tare da tura mutanen inda ya dace domin ganin sun girbi abinda suka shuka.



