Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta tsare matashin da ake zargi da kashe matar mahaifinsa saboda tana yi masa ihu a kunne a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta tsare matashin da ake zargi da kashe matar mahaifinsa saboda tana yi masa ihu a kunne a Kano.

Kotun majistret mai lamba 29 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Bashir Yusuf, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali bisa zargin sa da kashe matar mahaifinsa.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, matashin ya kashe Hajara Isah wadda abokiyar zaman mahaifiyarsa ce.

Matashin mai suna Halifa Miko ya bayyana wa kotun cewa, idan yaje ya yi dakon rogo ya dawo gida dan ya huta sai kawai matar baban nasa da zo dai-dai kunnen sa ta dinga yi masa ihu a kunne, shi kuma ga shi ya na son ya huta.

Matashin ya ci gaba da cewa, ya yi amfani da ɗanbuda ya kashe ta domin ya samu ya miƙe kafarsa ya huta.

A yayin zaman kotun na ranar Litinin 12 ga watan Oktoba, 2026, kotun ta aike da shi gidan gyaran hali zuwa wata ɗaya domin a ƙara gabatar da shi a gaban kotun.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, laifin da ake zargin matashin ya saɓa da sashi na 221 wato dai sashin nan mai ban tsoro.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM