Ƴan sandan Kano sun kama CSP na bogi da ake zargin yana cutar mutane

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da laifin sojan gona da cutar mutane a jihar.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Talata 8 ga watan Satumba, 2026.
A cewar sa, "Mutumin mai suna Adamu Musa mazaunin unguwar Kureƙen Sani a Kano, ana zargin sa da laifin yin sojan gonar, in da yake cewa shi babban Sifirtanda ne shi na yansanda wato (CSP)," in ji Kiyawa.
Ya kuma bayyana cewar za su gurfanar da mutumin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kan sa.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Kiyawa ya kuma buƙaci al'umma da su dinga saurin sanar da hukuma da zarar sun ga abin da suke da kokwanto a kansa.



