Koma Labarai
Tsaro

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malaman da suka je yi wa Tinubu addu'ar samun nasara.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malaman da suka je yi wa Tinubu addu'ar samun nasara.

Rundunar yansandan jihar Zamfara ta ce ta fara bincike, domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talatar Mafara a Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa lokacin da aka sace malaman, suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.

Yansandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu yan bindiga ɗauke da makamai suka yi wa wata mota da ke ɗauke da waɗanda lamarin ya rutsa da su kwanton ɓauna.

Ready to PlayDala FM88.5 FM