NSCDC ta kama Rayyanu Ibrahim bisa zargin lalata wayar wutar lantarki mai sulke a Jigawa.

Rundunar tsaro ta Civil Defense ta jihar Jigawa, ta kama Rayyanu Ibrahim, mai shekaru 35, bisa zargin sa da lalata wayar wutar lantarki mai sulke "Armour Cable" a tashar ruwa da ke ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta jihar.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar a jihar, Badureddeen Tijjani Mahmud, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Talata 22 ga watan Satumba, 2026.
Sanarwar ta ce, an gano ɓarnar da mutumin ya yi ne da ƙarfe 04:00 na safiyar ranar Lahadi 20 ga watan Satumba, 2026.
A cewar Badureddeen, bayan samun rahoton barnar ne jami'an rundunar na Birnin Kudu, suka fara gudanar da bincike, inda suka samu bayanan sirri daga wata ƙungiya mai rajin wanzar da zaman lafiya da tsaro, da ta taimaka wajen kama Rayyanu.
Sanarwar ta ce, binciken farko ya gano cewa, an lalata wasu sassa na tsarin wutar lantarkin gidan ruwan da ke Birnin Kudu.
Hukumar ta ce wanda ake zargi da aikata laifin ya amsa cewa yana da hannu a cikin lamarin, inda ya bayyana cewa yana sayar da irin waɗannan manyan wayoyin wutar lantarki ga ƴan Gwangwan.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, yanzu haka hukumar ta Civil Defense ta jihar Jigawa, ta faɗaɗa bincike domin gano mutanen da ke da hannu wajen aikata wannan laifin a birnin Kudu.
Kwamandan hukumar Civil Defense ta jihar Jigawa, Muhammad Kabiru Ingawa, ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da kare mahimman kadarorin Gwamnati da kuma kayayyakin al'umma.



