Koma Labarai
Tsaro

Ya kamata gwamnati a ƙarawa hukumomin tsaro kayan aiki don yaƙi da matsalar tsaro a Kano - Human Right

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ya kamata gwamnati a ƙarawa hukumomin tsaro kayan aiki don yaƙi da matsalar tsaro a Kano - Human Right

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives ta ƙasa, ta buƙaci Gwamnatin Kano da ta ƙara bai wa jami’an tsaro da hukumomin da ke yaƙi da miyagun ayyuka a jihar nan kayan aiki na zamani, domim gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar a matakin ƙasa, Kwamared Tasi'u Idris Idris Soja, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM a ranar Laraba 20 ga Agustan 2026, lokacin da yake tsokaci kan irin matakan da gwamnatin Kano, ke ɗauka wajen yaƙi miyagun ayyuka a jihar.

Ya ce ɗaukar wannan mataki da gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi abin yabawa ne, domin al’umma na buƙatar zaman lafiya, da tsaro da kwanciyar hankali domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

Sai dai Kwamared Tasi'u Soja ya ce, akwai buƙatar gwamnatin jihar Kano ta ƙara wa jami'an tsaron kayan aiki, musamman ma ga Ƴan Sanda, da jami'an rundunar tsaron da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da shaye-shayen kayan maye ta Anti-Phone Snatching Force, da kuma NDLEA, da Ƴan Bijilante da dai sauransu, domin ƙarfafa musu gwiwa a aikin.

Tasi'u ya kuma buƙaci al'umma da su ƙara baiwa hukumomin tsaro haɗin kan da ya dace ta yadda za su ƙara samun dama wajen daƙile miyagun ayyuka a sassan jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM