Mazauna garin Yadakunya sun zargi wani mutum da sayar da filin asibitin Bela ga wani kamfani a Kano

Wasu matasa sun yi kukan cewar wani mutum ya haɗe gonar sa da filin asibitin Bela, inda ya sayar wa wani kamfanin haƙar ƙasa, tare da fara haƙa musu kududdufi a garin Yadakunya da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Kano.
Shugaban ƙungiyar ci gaban garin na Yadakunya, Kwamarad Bala Yadakunya, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma'il, a ranar Alhamis 11 ga Yuni, 2026.
Kwamared Bala ya kuma ce haƙa wannan kududdufi zai kawo musu koma baya ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, lafiya da ilimi domin idan an haƙa kududdufin makarantar jan baki College, ma ba za a samu hanyar zuwan ta ba.
Sai dai wanda suke zargin mai suna Buhari Liman Kadiyawa, ya bayyana cewar babu filin asibiti a wannan waje inda ya ce duka gonarsa ce da ya saya a hannun mutane.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya tuntubi shugaban ƙaramar hukumar Ungogo ta wayar tarho, tunda dai an ce ya san da maganar, sai dai ya bayyana cewar ya yi bulaguro kuma da zarar ya dawo zai magantu.



