Zargin kisan kai: Gwamnatin Kano ta gurfanar da wani jami'in soja bisa zargin sa da kashe ɗan Karota.

Babbar Kotun jahar Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari'a A'isha Mahmud, ta ci gaba da sauraron shaidu a ƙunshin tuhumar da gwamnatin jaha ta ke wa wasu mutane uku ciki har da wani jami'in soja, kan zargin kashe ɗan Karota.
Lauyan gwamnati Lamiɗo Abba Soron ɗinki ya bayyana wa kotun cewar, a ranar 24 ga watan Mayu, 2025, da misalin ƙarfe uku na yamma waɗanda ake tuhuma da suka haɗar da Lansi kofur Tunde Momodu mai lambar aiki 19NA/74/3963, da Yakubu Abdussalam, da kuma Sagir Yusuf, a unguwar Mariri, sun haɗa baki sun kashe wani jami'in Karota ta hanyar soka masa wuƙa.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, waɗanda ake zargin sun zo shigewa kuma basu da takardun izinin yin lodi a don haka jam'i'in karotar ya buƙaci su tafi ofis, sai dai a kan hanyar su ne kuma aka zargi cewar sun soka masa wuƙa.
A zaman kotun na ranar Talata 28 ga Yuli, 2026, lauyan gwamnati Lamiɗo Soron ɗinki ya gabatar da wukar da aka yi kisan da ita da kuma hoton gawar marigayin, sai kuma takardun gwajin likitoci a matsayin shaidar nuni.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, zargin da ake yi wa mutanen ya saɓa da sashi na 221 na kundin penal code.



