Wanzamai ku zamanantar da sana'ar ku tare da yaƙi da masu batsa yayin tallan magungunan su a Kano - Hukumar Shari'a

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta buƙaci wanzamai da ke jihar nan, da su ƙara zamanantar da sana'ar su tare da ƙoƙarin cire dukkan baragurbi a cikin su saboda yadda Muslunci yake kare lafiya da rayuka da dukiyoyin jama'a.
Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ne ya bayyana hakan, lokacin da tawagar Sarkin Askar Kano, Alhaji Muhammad Yunusa Na Bango, suka ziyarci hukumar shari'ar, domin tattaunawa a kan mahimmancin batutuwa.
Cikin abubuwan da suka tattauna sun haɗar da matsalolin da ake fuskanta a tsakanin al'umma a sassan jihar, musamman kan illar shaye-shayen kayan maye, da faɗan daba, da kuma rashin tsaro, da hanyoyin da za a ƙara zamanantar da harkar wanzanci da tsaftace tallan magungunan gargajiya a tsakanin al'umma.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma ƙara da cewa, akwai buƙatar a ƙara zamanantar da harkokin wanzanci wanda zai yi dai-dai da zamani, duba da yadda komai yanzu ke tafiya a zamanance, domin samun ci gaban da ya dace.
Ya kuma buƙaci Sarakunan askar Kano da su ba da dukkan gudummawar su a harkar tsaro, domin ganin an yaƙi harkokin faɗan daba, da ƙwacen waya da kuma sha da dillancin kayan maye a sassan jihar.
A cewar sa, "Mun buƙaci tawagar Sarkin Askar, da su je su tsawatar wa dukkan masu magungunan gargajiya da ke bayyana batsa a yayin tallan magungunan su, a gefen tituna da cikin unguwanni, domin ƙara tsaftace harkar," in ji Ɗanabba.
Da yake nasa jawabin, Sarkin Askar Kano, kuma shugaban Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu magungunan gargajiya na ƙasa, Muhammad Yunusa Na Bango, ya ce sun kai ziyarar ne bayan da hukumar ta gayyace su domin zama wajen tattauna mahimman batutuwa.
A cewar sa, a yayin ziyarar sun kuma ƙulla alaƙar aiki tsakanin su da hukumar Shari'ar, tare da bada tabbacin gudunmawar da za su bayar ta ɓangarori daban-daban domin samun cigaba da jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.
Dukkanin ɓangarorin biyu dai sun sha alwashin ci gaba da bakin ƙokarin su wajen ganin an ƙara samun ci gaba a faɗin jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.



