Yanzu-yanzu: Kotun ƙoli ta soke taron jam’iyyar PDP na Ibadan da aka zaɓi Tanimu Turaki
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni na bayyana cewa kotun Koli ta yanke hukunci, inda ta soke babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025, da ta gabata.
Kafar yaɗa labarai ta Vanguard ta rawaito cewa, taron ne ya haifar da ɓangaren shugabancin ƙasa karkashin jagorancin Tanimu Turaki, wanda ke da’awar jagorantar jam’iyyar a wani ɓangare.
Kazalika, da wannan hukunci, bangaren da Turaki ke jagoranta ya gamu da koma baya, yayin da kotun ta bayyana taron a matsayin mara inganci a hukumance.
Majiyoyin labarin sun ambato cewa, a na sa ran ƙarin bayani kan dalilan hukuncin da kuma tasirinsa ga makomar jam’iyyar PDP zai biyo baya a nan gaba.



