Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta ɗaure matasa biyu shekaru 14 babu zaɓin tara a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta ɗaure matasa biyu shekaru 14 babu zaɓin tara a Kano

Babbar kotun jiha mai lamba 9 da ke zaman ta a Unguwar Bampai, Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Hadiza Sulaiman, ta ɗaure wasu matasa biyu, shekaru 14 babu zaɓin tara sakamakon samun su da laifin kisan kai.

Tunda fari dai gwamnatin jihar Kano ce ta gurfanar da matasan biyu da laifin haɗa baki da kisan kai.

Matasan sun haɗar da Nafi'u Garba, da Abdulmajeed Garba, mazauna unguwar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar a ranar 16 ga watan uku na shekarar 2019, da misalin karfe 08:15 na dare, wanda aka kashe mai suna Surajo, ya kasa matashin Nafi'u Garba a wajen neman aure lamarin da bai yi masa daɗi ba.

An yi zargin cewar Nafi'u Garba, ya ɗebo tarin wasu matasa inda suka yi wa Marigayi Surajo kisan gilla, har ya baƙunci lahira.

A yayin zaman kotun na ranar Litinin 27 ga watan Afrilu, 2026, mai gabatar da ƙara lauyan gwamnati Lamiɗo Abba Soron Ɗinki, ya gabatar da shaidu guda uku, yayin da waɗanda ake tuhuma suka kare kan su, inda nan take kotun ta yi watsi da shaidun kariya.

Kotun ta kuma bayyana cewar shaidun masu gabatar da ƙarar shaidu ne da suke gamsassu, a don haka ne ma kotun ta ayyana cewa ta samu matasan da laifin haɗin kai wajen haɗa baki da kisan kai.

Sai dai bayan nazari kotun ta ayyana cewa ta canza lambar tuhuma daga sashe na 221, zuwa sashe na 224, inda aka ayyana cewar lokacin da aka gurfanar da matasan shekarun su goma sha shida-shida.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kasancewar faɗa su ka yi da shi Marigayin ba haka siddan aka yi kisan ba, a don haka ne kotun ta canza lambar tuhumar, tare da ɗaure su aƙalla shekaru 14 a gidan ajiya da gyaran hali babu zaɓin tara.

Ready to PlayDala FM88.5 FM