Makuwar kuɗi: Kotu a Kano na neman Ishaq Mamman da ya bayyana a gaban ta

Kotun majistret mai lamba 24 mai zaman ta a Airport ɗin Mallam Aminu Kano, ta nemi Ishaq Mamman da ya bayyana a gaban ta a ranar Litinin mai zuwa.
Tun da farko wani mutum ne mai suna Isa Bila Yahaya, ya shigar da ƙara yana ƙarar Ishaq Mamman, da wani banki bisa tura wasu kuɗaɗe a banki.
Tun a ranar 22 ga watan ɗaya na wannan shekarar ta 2026, ne Isa Bila Yahaya ya tura da kuɗin asusun ajiya na Ishaq Mamman.
Kasancewar an kasa samun Ishaq Mamman din lauyoyin mai ƙara suka roƙi kotun da a neme shi ta kafar yaɗa labarai, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito.
Kotun ta kuma umarci Ishaq Mamman da ya gabata a gaban ta a ranar Litini 27 ga watan Afrilu 2026, idan yaƙi za ta yi umarni ga bankin su mayar wa mai kuɗin haƙƙin sa, suma kuma bankin an tura musu su gabata a ranar Litinin ɗin a kotun.



