Kotu ta yanke wa Umar Idris Farawa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da laifi

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 16 Ƙarƙashin jagoran mai shari'a Sanusi Ado Ma'aji, ta ayyana hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani matashi mai suna Umar Idris Farawa.
Gwamnatin jahar Kano ce dai ta gurfanar da matashin bisa zargin sa da kutse, da sata da kisan kai.
Lauyan gwamnati Lamiɗo Soron dinki, ya gabatar da shaidu uku a gaban kotun inda shi kuma Umar ya kare kansa da kansa.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar a ranar 27 ga watan September 2021, Umar ya shiga shagon wani matashi mai suna Abubakar ya sace masa kayan lefe, a yayin da yake yunƙurin tserewa sai suka yi kiciɓis da mai shagon gudun kada asirinsa ya tonu sai ya zaro wuka ya burma masa a wuya lamarin da ya yi dalilin mutuwar sa.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar, kotun ta gamsu da shaidun mai gabatar da ƙara, an kuma yi watsi da shaidun kariya a don haka kotun ta ayyana hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin.



