Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta ɗaure matashin da ya bijirewa kamun ƴan sanda bayan samun sa da laifi daban-daban a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta ɗaure matashin da ya bijirewa kamun ƴan sanda bayan samun sa da laifi daban-daban a Kano

Kotun majistret mai lamba 24 da ke zamanta a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Muttaƙa Abba Ɗandago, ta hori matashi Ibrahim Garba Rijiyar Lemo, da ɗaurin wata ɗaya a gidan gyaran hali babu zabin tara a laifin cin zarafi.

Kotun ta kuma ɗaure matashin wata ɗaya babu zaɓin tara a laifin sanadin rauni, da kuma wata biyu babu zaɓin tara a laifin samu da miyagun kwayoyi.

Kazalika, kotun ta yi wa Ibrahim Garba ɗaurin wata biyu babu zaɓin tara a laifin samu da makami, da kuma ɗaurin watanni 6 ko tarar dubu 50 a laifin tayar da hankalin al'umma.

Har ila yau, kotun ta hori matashin da ɗaurin watanni 7 ko kuma ya biya kuɗin ramko na naira dubu 100 ga mutane 2 da ya ji wa rauni, sai kuma wata ɗaya babu zaɓin tara a laifin bujirewa kamun ƴansanda.

Ana tuhumar matashin da laifuka 6 waɗanda suka haɗar da samu da makami, da sanadin rauni, da samu samu da miyagun kwayoyi, sai kuma cin mutunci da tayar da hankalin al'umma laifukan da ya amsa.

Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Mai Shari'a Muttaka Abba Ɗandago ya kuma umarci matashin da ya sanya hannu a kan yarjejeniyar zama mutumin kirki idan kuma ya kammala wa'adin da aka yanke masa zai dinga zuwa kotun tsawon watanno 6 din ganin ɗabi'unsa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM