Ba za mu lamunci tayar da hankalin al'umma ba a Kano - Kotu.

Kotun majistret mai lamba 24 mai zaman ta a Airport ɗin Mallam Aminu Kano, ƙarkashian jagoran mai shari'a Muttaƙa Abba Ɗandago, ta fara sauraron wata shari'a wadda ƴansanda suka gurfanar da wasu matasa da ake zargi da laifin haɗa baki da tayar da hankalin al'umma, da yawon banza da kuma samu a haramtaccen guri.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, gungun matasan an kama su ne a unguwar Badawa suna tsaka da tayar da zaune tsaye.
A zaman kotun na yau Juma'a 24 ga watan Afrilu, 2026, dukkanin matasan sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.
Lauyoyin matasa biyar daga cikin su sun roƙi a sanya su a hannun beli, inda nan take kotun ta amince da roƙon, an sanya matasa biyar a hannun beli bisa sharaɗin mai matakin albashi na 16, da kuma ɗan uwansu na jini da kuma limamin coci wato Pastor.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar, matasan da ake zargin sun haɗar da Henry Genus, Gabriel Mathis, Abraham Daniel, Goodwill Emanuel, Dominic Felix, da kuma Peter Onbe, Destring Edelium.
Sauran sun hadar da Felix Uban, ID Emanuel, Poul Ager, Peter Morphy, Mathius Odion, Adams Angeler sai kuma kallabi tsakanin rawuna Mery Joseph.
Kotun ta kuma ce ba za ta lamunci tayar da hankalin al'umma ba a Kano.
Kotun ta ce a tafi da matasan gidan gyaran hali zuwa ranar 25 ga watan gobe, idan har suka gaza cika sharaɗin belin.



