Koma Labarai
Tsaro

Da Ɗumi-Ɗumi: CP Bakori ya tura Ƴan Sanda 250 zuwa iyakokin jihar Kano bayan kammala ɗaukar horo.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Da Ɗumi-Ɗumi: CP Bakori ya tura Ƴan Sanda 250 zuwa iyakokin jihar Kano bayan kammala ɗaukar horo.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta tura jami'an ta guda 250 zuwa iyakokin Jihar Kano bayan kammala ɗaukar horo, domin gudanar da ayyukan tsaro.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a shafin sa na Facebook, ranar Talata 1 ga watan Satumban 2026.

Ya ce Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayar da umarnin tura jami'an domin gudanar da ayyukan tsaro a iyakokin jihar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM