Babban mai taimakawa Gwamnan Kano kan asibitin tafi da gidanka Ibrahim Mua'zu Gama ya rasu.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Allah ya yi wa babban Mai taimakawa Gwamnan Kano a kan harkokin asibitin tafi da gidanka "Medical outreach" Hon. Ibrahim Mu'azu Gama, rasuwa.
Alhaji Ibrahim Mua'zu Gama ya rasu a yammacin Larabar nan bayan gajeriyar rashin lafiya.
Za a yi jana'izar sa a gobe Alhamis da misalin ƙarfe 09:00 na safe, a layin Takari da ke unguwar Gama a karamar hukumar Nasarawa, inda za a kai shi maƙabartar Ahmadiyya.



