Kotu ta yanke wa Alhaji Umar Idris ɗaurin sati 2 da biyan tarar dubu 100, bisa ajiye buhunan bahaya cikin unguwa a Kano

Kotun Majistare mai lamba 7 da ke zamanta a Norman’s Land, ta yanke wa Alhaji Umar Idris hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon mako biyu tare da biyan tarar naira dubu ɗari 100,000.
Kotun ta yanke masa hukuncin ne bisa samun sa da laifin cutar da al’umma da kuma jefa lafiyar jama’a cikin haɗari sakamakon jibge buhunan kashin mutane a ƙofar gidansa da ke unguwar Kurna Farin Bebe.
Bayan karanta masa kunshin tuhumar, wanda ya amsa laifinsa, mai gabatar da ƙara, Barista Bahijja H. Aliyu, ta roƙi kotun da ta yanke masa hukunci nan take.
Kotun ta amince da buƙatar tare da yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na mako biyu da kuma biyan tarar naira dubu 100,000.
Tun da farko, Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta shigar da ƙarar bayan samun rahotannin cewa an jibge buhunan kashin mutane a ƙofar gidan wanda hakan ke haifar da barazana ga lafiya da kuma gurɓata muhalli a yankin.



