Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama Sadeek Muhammad kan zargin cakawa direban Adai-daita sahu wuka a Ɗorayi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta kama Sadeek Muhammad kan zargin cakawa direban Adai-daita sahu wuka a Ɗorayi

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force Kano, ta kama wani matashi Sadeek Muhammad, bisa zargin sa da cakawa direban Adai-daita sahu wuka a gefen Ƙugun sa, a unguwar Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Kwamandan rundunar tsaron a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya sanar da kama matashin yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce binciken su ya gano cewa matashin ya cakawa direban Adai-daita sahun wuƙar ne a lokacin da suka je yi masa ƙwacen waya a yankin na Ɗorayi, inda abokan sa suka kwashe wa direban kuɗin cinikin da ya yi.

Nura Salisu Sharaɗa ya kuma ce sun samu matashin da ƙwayoyi da ake kira Fara, guda 40, da Fiji guda uku, da kuma Diyaza kati uku da rabi, waɗanda yake sayar wa a unguwar Ɗorayi.

Da yake ƙarin bayani ga gidan rediyon Dala FM Kano, matashin da aka kama Sadeek Muhammad ɗan shekaru 19, mazaunin unguwar Dorayi, ya ce da yardar Allah ya daina riƙe wuƙa, da kwacen waya da kuma sayar da ƙwayoyin domin tsira da mutuncin sa.

Sai dai Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snatching Force Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya ce za su miƙa matashin inda ya dace domin ɗaukar matakin da ya dace a kan sa.

Ya kuma gargaɗi dukkanin matasan da suke addabar mutane da miyagun ayyuka a sassan jihar Kano, da su daina tare da yin watsi da makamansu domin duk wanda ya shiga hannun su da aikata laifi ba zai ji da daɗi ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM