Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano na shirin kafa kamfanin jiragen sama mallakin jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano na shirin kafa kamfanin jiragen sama mallakin jihar

Gwamnatin Kano ta tana duba yiwuwar kafa kamfanin jiragen sama mallakin jihar, domin faɗaɗa hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi da inganta harkokin sufuri da kuma samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga alhazan Jihar Kano a birnin Makkah.

Ya kuma ce kafa kamfanin jiragen saman zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci, da sauƙaƙa zirga-zirgar jama'a da kuma ƙara wa jihar damar samun kuɗaɗen shiga.

Ready to PlayDala FM88.5 FM