Ba za mu yi zaɓe ba a 2027, idan ba a magance ƙalubalen yankin mu ba - Mazauna Gyaranya lungun Fatake a Kano

Al'ummar unguwar Gyaranya lungun Fatake, da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, sun gudanar da tattaki domin tunatar da shugabannin yankin su, lalacewar magudanar ruwansu wanda ke haifar musu da ambaliyar ruwa.
Mazauna unguwar sun ce sun haura shekaru 23 suna fama da lalacewar magudanar ruwan, kuma sun sha bibiya ga mahukuntan yankin domin ganin an gyara musu ita amma lamarin ya ci tura.
A cewar su lalacewar da magudanar ruwan nasu ta yi na sanya su cikin furgici, musamman ma a lokacin damuna domin kuwa duk lokacin da hadari ya taso hankalinsu na matukar tashi bisa yadda ruwan sama ke shiga cikin gidajen su.
Sun ce damuwar da suke ciki a kan lamarin hakan ne ya sa suka fito a ranar Lahadi 7 ga Yuni, 2026, inda suka gudanar da tattaki domin kira ga mahukunta kan su kai musu ɗauki.
Da yake jawabi ga Dala FM Kano, shugaban ƙungiyar samar da ci gaban yankin, ta Gyaranya Nagartacciya, Abdussamad Tijjani Musa, ya ce tura ce ta kai bango ya sa suka gudanar da tattakin domin nusar da mahukunta ƙalulaben da yake damun su na rashin magudanar ruwan.
Ya kuma ce mutanen unguwar sun ce yanzu haka ba za su yi zaɓe ba a 2027, matuƙar ba a samar musu da magudanar ruwa a unguwar Gyaranya lungun Fatake ba, a don haka suka bukaci a yi musu aikin ko su ƙauracewa yin zaɓen.
A cewar sa, "Baya ga matsalar lalacewar magudanar ruwa, akwai ƙalubalen da ke damun mu na ƙarancin al'amuran more rayuwa, irin su Asibiti, ruwa, da batun ilimin da dai sauran su, in ji Abdussamad.”
Malama Usaina Salisu Gyaran, dattijuwa ce da ke zaune a unguwar Gyaranya lungun Fatake, ta ce babban burinsu shi ne gwamantin Kano ta kai musu ɗauki, tunda dai shugabannin yankin nasu sun gaza fitar da su kunya daga halin da suke ciki.
Da yake jawabi, tsohon Kansilan Mazaɓar Unguwar Gyaranya lungun Fatake, Ali Wada Turaki Aliko Anas, ya ce a matsayin su na guda daga cikin Kokas na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Gwale, za su miƙa koken al'ummar yankin ga shugabanninsu.



