An yi jana'izar Kakakin Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni na bayyana cewa kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya rasu a Kano.
Shugaban shiyyar hukumar na karamar hukumar Dambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru, ya tabbatar da rasuwar ga manema labarai a ranar Laraba 07 ga watan Oktoba, 2026.
Ya ce Marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen isar da bayanai ga al’umma dangane da ayyukan hukumar, da kuma abubuwan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Tuni aka yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Laraba 7 ga watan October 2026 a jihar Kano.
Al'umma da dama ne dai ke ci gaba da bayyana alhinin su dangane da rasuwar Marigayi ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, tare da addu'ar Allah ya jiƙansa da gafara.



