Sojan bogi ya shiga hannun jami'an tsaro a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kama wani mutum da ake zargin sojan bogi ne a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, yayin wani sintiri da dakarunta suka gudanar a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce dakarun Brigade ta 17 sun kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana a ranar 4 ga Yuli, 2026, bayan sun gan shi sanye da gajeren wando irin na kayan sojoji, lamarin da ya sa suka tsayar da shi domin bincike.
Sanarwar ta ce, binciken da aka gudanar ya kai ga gano katin shaidar aikin soja na bogi, da katunan ATM guda huɗu, gajeren wandon kayan sojoji, da agogon hannu da kuma kuɗi Naira 17,000 a hannunsa kamar yadda TVC News ta ruwaito.
Rundunar ta kuma ce an tsare wanda ake zargin ne tare da kayayyakin da aka ƙwace, domin ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin kafin ɗaukar mataki na gaba.



