NASENI ta sake ƙaddamar da rabon na'urar ƙyanƙyasar kaji da kayan gyaran wutar lantarki ga matasa a Kano

Hukumar inganta harkokin kimiyya da fasaha ta ƙasa NASENI, ta sake ƙaddamar da rabon na'urar ƙyankyasar kaji da wasu kayayyakin gyaran wutar lantarki ga matasa a jihar Kano.
Shugaban hukumar Mallam Khalil Sulaiman Halilu, ya bayyana cewar sun ɗauki matakin tallafawa matasa ta hanyar basu horo domin kawo ƙarshen barace-barace a jihar.
Da take bayani a wajen taron, shugabar Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Kano, ALGON, Hajiya Sa'adatu Yusha'u, ta miƙa godiyar ta ga hukumar bisa yadda take tallafawa matasa a harkokin sana'a a faɗin jihar Kano.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, taron da aka gudanar yau Asabar a Kano, ya samu wakilci daga ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da sakataren gwamnatin tarayya, da kuma wakilai daga ɓangaren gwamnatin jahar Kano.



