Koma Labarai
Labarai

Za mu ɗauki nauyin kula da iyalan marigayiya Ummulkhairi da aka yi wa kisan gilla a mararrabar Jos - Gwamnan Kaduna

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Za mu ɗauki nauyin kula da iyalan marigayiya Ummulkhairi da aka yi wa kisan gilla a mararrabar Jos - Gwamnan Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu, wacce wasu fusatattun mutane suka kashe a garin Maraban Jos da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayiyar, a ranar Asabar 27 ga Yuni, 2026.

Ya ce gwamnatin jihar za ta rinƙa kula da rayuwar mijin marigayiyar da 'ya'yanta huɗu, tare da ɗaukar nauyin karatun yaran har zuwa matakin da ya dace.

Uba Sani ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa iyalan marigayiyar tare da tabbatar da cewa an yi adalci kan lamarin, kamar yadda kafar Daily Post Nigeria ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan gillar da aka yi wa Malamar makarantar islamiyyar, Marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM