Koma Labarai
Shari'a

Da Ɗumi-Ɗumi: DSS ta ba da umarnin binciken jami’an ta da suka ja Sowore a Kotu

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Da Ɗumi-Ɗumi: DSS ta ba da umarnin binciken jami’an ta da suka ja Sowore a Kotu

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS ta ba da umarni a gudanar da bincike kan jami’anta da aka gani suna jan ɗan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, bayan zaman kotu a Abuja.

Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje, a ranar Talata 23 Yuni, 2026, har sai an saurari ƙarar da ya shigar kan soke belinsa, kamar yadda kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Alƙalin kotun Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan ya yi watsi da buƙatar Sowore ta janye kansa daga shari’ar bisa zargin nuna son kai.

Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna wasu jami’an DSS masu ɗauke da bindigogi suna jan Sowore daga harabar kotu, lamarin da ya jawo suka daga al'umma.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun DSS, Favour Dozie, ya ce shugaban hukumar ya ba da umarnin gaggauta bincike kan halayen jami’an da abin ya shafa.

Ya kuma ce Sowore ne da kansa ya zaɓi shiga motar DSS maimakon ta hukumar gidajen gyaran hali bayan faruwar lamarin.

DSS ta ce tana tuhumar Sowore ne saboda wasu kalamai da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ake zarginsa da kiran Shugaba Bola Tinubu “mai laifi”.

Hukumar ta ce tun a shekarar 2025, ta nemi ya janye kalaman nasa kafin daga baya ta kai ƙarar sa kotu domin neman fassarar doka kan haƙƙin yin irin waɗannan kalamai kan shugaban ƙasa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM