Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta fara rangadi zuwa tashoshin mota da kasuwanni don tsaftace kasuwanci da magance matsaloli a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta fara rangadi zuwa tashoshin mota da kasuwanni don tsaftace kasuwanci da magance matsaloli a Kano.

Hukumar Shari'ar ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta fara wani rangadi a tashoshin mota, da kasuwanni domin ƙulla alaƙar aiki tare da tsaftace kasuwanci da magance matsalolin da ke damun jama'a ta ɓangarorin.

Tawagar hukumar ta fara kai ziyarar ne da tashar mota ta Kano Line da ke Na'ibawa, da kasuwar sayar da kayan marmari ta Na'ibawa, da kuma Cibiyar magunguna da ke Ɗangoro, a ranar Laraba 07 ga watan Oktoba, 2026.

Da yake ƙarin bayani, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce a yayin ziyarar sun faɗakar da al'ummomin da ke cikin tashoshin motar da kasuwannin, la'akari da yadda suke haɗa mutane daban-daban, domin ganin an ƙara samun tsafta da zama lafiya a jihar Kano.

A cewar sa, "Fatan gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, shi ne a kawar da shan miyagun ƙwayoyi, da kawo gyara a harkokin tuƙi, da kuma gyaruwar tarbiyyar matasa, a don haka hukumar shari'ar ta ɗauki gaɓarar aiwatar da hakan," in ji Ɗanabba.

Shima da yake nasa jawabin, shugaban hukumar sufuri ta Kano Line, Yunusa Ibrahim, ta hannun wakilcin da ya samu na mataimakin sa Haladu Musa, ya ce a shirye suke wajen ganin direbobinsu sun yi amfani da faɗakarwar da hukumar ta yi musu.

Usaini Labaran Zakari shi ne Manajan Darakta na Cibiyar sayar da magani ta Kanawa da ke Ɗangoro, ya miƙa godiyar su ga hukumar shari'ar bisa ziyarar aikin da ta kai musu.

Shima a nasa ɓangaren, Sarkin kasuwar sayar da kayan marmari ta Na'ibawa, Mallam Abubakar Adam, da Sakataren ƙungiyar kasuwar Adamu Muhammad, sun ce za su yi duk mai yiyuwa domin yin amfani da duk abinda suka ji daga hukumar Shari'ar.

Tunda farko, Kwamishina na ɗaya a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Gwani Muhammad Hadi Yakasai, ya buƙaci shugabannin kasuwanni da na tashoshin mota, da su tausayawa na ƙasa dasu domin ganin sun samu ci gaban da ya dace.

A yayin ziyarce-ziyarcen Kwamishina na ɗaya da na biyu na hukumar shari'ar sun samu rakiyar wasu daga cikin daraktoci, da kuma shugabannin hukumar da dama.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM