Kotu ta ɗaure Zainab watanni biyar tare da bulala 10, bisa zagin Hisbah da Kwamandan hukumar a Tiktok..

Kotun shari'ar Musulunci da ke Sharaɗa, harabar shelkwatar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta yanke wa ƴar TikTok ɗin nan Zainab Abubakar, ’yar shekaru 19, hukuncin ɗaurin watanni biyar a gidan yari da bulala 10 ba tare da zaɓin tara ba, bayan ta amsa laifin zagin Hisbah da Kwamandanta.
A yayin zaman kotun da Mai Shari’a Bashir Abdullahi Ibrahim ya jagoranta a yau Laraba, an gurfanar da Zainab tare da wasu mutane biyu da Hukumar Hisbah ta kama bisa zargin cin zarafin hukumar da Babban Kwamandanta a TikTok.
An tuhumi Zainab da aikata laifin zagin wanda ya saɓa wa sashe na 312 na dokar Penal Code, inda ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi kafin kotun ta yanke mata hukunci, kamar yadda kafar Arewa update ta ruwaito.
Sauran mutanen biyu, Ahmad Usman wanda ake kira Ortega, ɗan shekara 25, da Muhammad Aliyu, ɗan shekara 20, sun musanta tuhumar haɗa baki da zagin Hisbah da Babban Kwamandanta, Malam Aminu Ibrahim Daurawa.
Bayan lauyansu ya nemi a bayar da belinsu, kotun ta tura su gidan yari na tsawon makonni biyu domin duba yiwuwar beli, tare da umartar mai gabatar da ƙara ya shirya gabatar da shaidu.



