Kotu ta tabbatar da Tijjani Gandu a matsayin ɗan takarar NDC na Kano Municipal
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da ƙarar da Hon. Aminu Ishak Yusif ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Hon. Tijjani Husaini Gandu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar NDC a Ƙaramar Hukumar Birnin Kano.
Mai Shari’a Simon Amobeda ne ya jagoranci zaman kotun da ta kori ƙarar, bayan mai ƙarar ya kasa gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa ya sayi fom ɗin takara ko kuma ya shiga zaɓen fidda gwanin jam’iyyar.
Hukuncin ya tabbatar da nasarar Tijjani Husaini Gandu a zaɓen fidda gwanin na jam’iyyar NDC a mazaɓar Birni, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.



