Ƙungiyar Astute Civil Society ta buƙaci INEC, ta gaggauta saka sunayen Aminu Gwarzo cikin ƴan takarar gwamna a Kano.

Ƙungiyar ƴan kishin ƙasa ta Astute Civil Society for Cultural and Humanity Development, ta nuna damuwar ta kan cire sunayen wasu ƴan takararkari da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta yi a sunayen ƙarshe da ta fitar.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a sakatariyar ƴan Jarida ta jihar Kano, a ranar Asabar 17 ga watan Oktoba, 2026.
Daga cikin ƴan takarar da ƙungiyar ta nuna damuwa kan cire sunayen su a hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, akwai ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdulssalam Gwarzo, da mataimakin sa Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso.
Kazalika, ta kuma bayyana damuwa kan cire sunayen ƴan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, na jahohin Gombe Farfesa Isah Ali Pantami, da mataimakin sa, da kuma na Ogun Oladipupo Ladi Adebutu.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa bai kamata hukumar ta cire sunan Kwamared Aminu Abdulssalam Gwarzo, da Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso, ba, daga cikin ƴan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar NDC, a don haka take kira da a gaggauta saka sunayen su.
Ta kuma bayyana cewa idan wani ɗan takara ko jam'iyya na da hujjojin da ke nuna an cire sunansa bisa kuskure, ya kamata hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta gudanar da bincike na musamman tare da ɗaukar matakin gyara idan har dokar hukumar ta bada damar hakan.
Ƙungiyar ta hannun jami'in yaɗa labaran ta, Kwamared Ibrahim Ali, ta bayyana cewa tana da masaniya a kan bayanin da hukumar INEC ta fitar na ƙarshe, wanda ta ce ta cire sunayen ƴan takarar yana da alaƙa ne da rashin cika wasu sharuɗɗan doka dangane da rajistar mambobin jam'iyyun siyasa, bayan wani hukuncin kotun ƙoli.
Sai dai ƙungiyar ta buƙaci hukumar INEC, da ta fito ta yi bayani ƙarara kan babban dalilin da ya sa ta cire sunayen ƴan takarar, tare da hujjoji.
ƙungiyar Astute Civil Society for Humanity Development, ta bayyana cewa ta yi wannan kiran ne domin ganin an tabbatar da gaskiya da adalci.
A cewar ta, "Kiran namu ba mu na goyon bayan wata jam'iyya ko wani ɗan takara ba ne, illa kawai don ganin an tabbatar da adalci da bin doka, da kuma ƙarfafa amincewar jama'a ga tsarin zaɓe," in ji ƙungiyar.
Haka kuma, Ƙungiyar ta yi kira ga ƴan siyasa, da magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki, da su guji kalaman tunzura al'umma, tare da bin hanyoyin doka wajen warware taƙaddamar cire sunayen ƴan takarar don tabbatar da zaman lafiya.



