Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da wasu gine-gine tare da rufe wasu da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta dakatar da wasu gine-gine tare da rufe wasu da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba.

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da wasu gine-gine tare da rufe wasu da ta ce an yi su ne ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban na cikin birnin jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ɗaukkowa gwamnan Kano rahoto Nanu Kankarofi ya fitar a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.

Kazalika, Sanarwar ta ce, tawagar kwamitin yaƙi da gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin kuma Shugaban hulumar KANGIS, Ɗalhatu Aliyu Sani, ce ta gudanar da aikin.

Sanarwar ta kuma ce tawagar ta dakatar da wasu gine-gine tare da sanya musu alama, yayin da aka rufe wasu da aka ce an gina su ba bisa ƙa’ida ba, musamman a kusa da magudanan ruwa a sassan jihar Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa, matakin na daga cikin aikin tabbatar da bin dokokin amfani da filaye da tsare-tsaren gine-gine tare da kare wuraren jama’a da magudanan ruwa a faɗin jihar, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM