Za mu daina aikin yaƙi da ɓata gari tun da gwamnati ta nuna ba ta so - Gamayyar Matasan Kano

Ƙungiyar Gamayyar Matasa Kano, ta yi barazanar dakatar da aiki na yaƙi da faɗan daba, da ƙwacen waya da shaye-shayen kayan maye, sakamakon yadda take samun rashin kulawa daga ɓangaren gwamnatin jihar.
Shugaban Ƙungiyar a matakin jihar Kano, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.
Ya ce sun gaji da yadda gwamnatin jihar Kano, ke nuna musu halin ko in kula, domin kuwa duk da irin ƙoƙarin da suke yi na aikin tabbatar da tsaro, da yaƙi da masu faɗan daba, da ƙwacen waya, shan kayan maye a jihar.
Ya kuma ce aƙalla sun rubuta sama da tarkarda guda goma, domin buƙatar ganin Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sakataren Gwamnatin jihar, don sanar da su hanyoyin da ya kamata abi domin dakile rikicin daba, a jihar, amma kawo yanzu shiru ba a kira su ba.
Ya ce rashin kiran nasu ya nuna musu cewa gwamnatin Kano ba ta buƙatar gudummawar da suke bayar wa a jihar, a don haka suka ga dacewar su daina tunda ba a so.
A cewar sa, "Kuɗin mu muke kashe wa, mu ke sayen kayan aiki, da zirga-zirgar ababen hawa, da kuma baiwa waɗanda muke aiki da su kuɗaɗe, sai dai rashin samun tallafin Kano, na matuƙar damun mu, don haka za mu daina, in ji MTD.”
Muhammad Tijjani Ɗorayi ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara kula da tarbiyyar ƴaƴansu domin gujewa fadawar su cikin al'amuran da basu dace ba.



