Koma Labarai
Labarai

Za mu mara baya ga duk ƙungiyar da ke son kawo ci gaba a Kano - Sarkin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Za mu  mara baya ga duk ƙungiyar da ke son kawo ci gaba a Kano - Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya bayyana cewa masarautar Kano  shirye take wajen marawa duk wata ƙungiya baya da za ta kawo cigaba a faɗin jihar Kano.

‎Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da ƙungiyar ƙwararrun sakatarori ta ƙasa da kuma reshen ta na Kano, wanda aka gudanar yau Alhamis 11 ga Yuni, 2026, a Kano.

‎Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya kuma bayyana jihar Kano da cewa, cibiyar kasuwanci ce a fadin Afrika, inda ya kuma taya ƙungiyar murna bisa cikar ta shekara sintin da kafuwa.

‎A nasa jawabin, sabon shugaban Ƙungiyar sakatarori da ƙwararru a aikin gwamnati ta ƙasa ICSAN, reshen jihar Kano, Barista Muhammad Na Sambo, ya yi alkawarin kawo cigaban da ya dace a ƙungiyar da ma jihar Kano.

‎Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, Farfesa Kamilu Sani Fagge da Farfesa Abdulmuminu Ahmed daga jami'ar bayero ne suka gabatar da mukala a wajen taron, wadda ta ƙunshi harkokin cigaban Kasuwanci a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM