Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta shiga cikin tsarin yadda ake bayar da hayar gidaje da shaguna a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta shiga cikin tsarin yadda ake bayar da hayar gidaje da shaguna a Kano.

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnatin Kano da ta shiga cikin tsarin yadda ake bayar da hayar gidaje da shaguna domin tsafta ce sana'ar a faɗin jihar.

A zaman majalisar na ranar Litinin 12 ga Octoba, 2026, bisa jagorancin shugaban majalisar Jibril Isma'il Falgore, ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Musa Ali Kachako ne ya gabatar da ƙudirin da nufin samun sauƙi ga al'ummar jihar nan.

Musa Ali Kachako ya ce, yanayin yadda mutane ke bayar da hayar gidaje da kuma shaguna ya saɓa da dokar bayar da haya ta jihar Kano.

Kachako ya ce idan gwamnati ta shigo cikin harkar za a samu damar tsaftace harkar, tare da samar da ingantaccen tsaro. Sannan ya ce kudirin baya nufin danne haƙƙin masu bayar da haya, sai dai illa samar da daidaito.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma ce za ta sake duba dokar bayar da haya tare da yi mata gyaran da ya dace.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM