Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya wajabta rashin shaye-shaye kafin naɗin dagaci ko mai unguwa a jihar.

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana cewa matuƙar maso a rage matsalar shan miyagun ƙwayoyi jihar nan dole ne sai an hana shigo da kwayoyin cikin Najeriya, tare da ɗaukar matakai tsaurara wajen sanya doka akan duk wani mai neman mukami sai an tabbatar baya mu'amala da miyagun kwayoyi.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Sumai'ila da Warawa Barista Rabi'u Yusuf, ya ziyarci shi, ƙarƙashin wani kwamiti da shugaban majalisar wakilai ta ƙasa ta kafa, don shawo kan ya waitar shan miyagun kwayoyi musamman tsakanin matasa maza da mata harma da matan aure.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu yace ta hak ne kadai za'a magance matsalar shan miyagun kwayoyi tsakanin al'umma musamman matasa.
Sarkin ya kara da cewa tuni masarautar Kano ta sanya doka duk wani mai unguwa ko dagaci da za'a nada sai an tabbatar baya shaye shaye kafin a nadashi.



