Gwamnan Kano ya jagoranci ɗaurin auren gata na mutane 3,000, ciki har da Haruna Bashir da aka yi wa iyalansa kisan gilla

Gwamnatin Kano ta gudanar da ɗaurin auren gata ga mutane 3,000, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance waliyyin malam Haruna Bashir, wanda aka yiwa iyalan sa kisan gilla a watannin baya a yankin Chiranci da ke yankin Ɗorayi.
Auren na Malam Haruna da amaryar sa Nabila Kabiru Yunusa, da sauran amare da angwayen, wanda ya gudana a fadar Sarkin Kano, Gwamna Abba Kabir ne ya zamo waliyyin angwaye yayin da Sarki Muhammad Sunusi na II ya zamo waliyyin amare.
Da yake jawabi a wajen ɗaurin auren, babban Kwamandan hukumar Hisba ta Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce ɗaurin auren ya gudana ne lokaci ɗaya da na sauran dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar,
Ya kuma ce a ƙarƙashin shirin, gwamnatin Kano ta bai wa kowace amarya naira dubu 100 a matsayin sadaki da naira dubu 100 a matsayin tallafin fara sana'a.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce gwamnatin Kano ta ɗauki matakai da dama domin tallafawa Haruna Bashir, ciki har da ɗaukar nauyin aikin Umrah da Hajjin sa, tare da ba shi gida a Amana City domin taimaka masa ya farfaɗo daga ibtila'in da ya fuskanta.
Wakilinmu na gidan Gwamnatin kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, Sheikh Daurawa ya yi kira ga sabbin ma'auratan da su gina zamantakewar aurensu bisa fahimtar juna, zaman lafiya da haƙuri da juna domin samun zuri'a dayyiba.



