Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da yunƙurin rushe tsohuwar gadar garin Watari da ke Kumbotso.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta dakatar da yunƙurin rushe tsohuwar gadar garin Watari da ke Kumbotso.

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wasu mutane da ke yunƙurin rushe tsohuwar gadar garin Watari a Kumbotso a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa gadar ta shafe fiye da shekaru hamsin al'ummar yankin da makiyaya na amfanar ta, yayin tsallaka babban titin domin kauce wa faruwar hatsari.

A cewar sa, "Ɗaukar matakin dakatarwar ya zo ne sakamakon ƙorafe-ƙorafen da al'ummar da ke zaune a yankin suka shigar ma'aikatar ƙasa da tsara birane, kan yadda wasu ke ƙoƙarin rusa gadar ba tare da yarjewar gwamnati ba, in ji shi".

Kwamishinan ma'aikatar kasa da tsara birane na jihar, Abduljabbar Muhammad Umar Garko ne, ya jagoranci aikin dakatar da rushe gadar tare da kama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Yayin da yake jawabi a wurin, kwamishinan ma'aikatar kasar ya bukaci al'umma, da su cigaba da sanar da su, duk wani aiki da ya saɓa da doka ga hukumomin da suka dace.

Ya kuma yi gargaɗin cewa wasu mutanen na yaudarar jama'a kan cewa suna da izinin gwamnati, alhali ba Su da wani izini daga ɓangaren gwamnatin.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, Kwamishinan ma'aikatar kasar Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ya kuma jaddada cewa, gwamnatin jihar Kano ba za ta amince da duk wani yunƙuri na lalata kadarorin al'umma ko na gwamnati ba, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a irin wannan badaƙala zai fuskanci fushin hukuma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM