Shugaba Tinubu ya ce matatun man fetur na Nijeriya za su dawo aiki yadda ya kamata.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ma’aikatan man fetur na kasar cewa matatun man Nijeriya da suka kwashe shekaru suna fama da rashin aiki yadda ya kamata, za su koma aikin su yadda ya kamata.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 13 ga watan Agusta, 2026.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta Nijeriya (NUPENG) a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.



