Na aurar da ƴaƴa 3, yanzu ina da ƴaƴa 10 da mata ɗaya, duk da sana'ar kwasar Turoso - Dattijo a Kano

Wani dattijo da ke sana'ar Kwasar Turoso mai suna Mallam Ibrahim Abdulhameed Gandun Albasa, ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar Kano ta rinƙa tallafa wa masu sana'ar da motocin aiki da sauran kayan aiki na zamani, domin ƙara bunƙasa sana'ar tasu, ta yadda za su ƙara taimakon rayuwar su da ma sauran al'umma.
Mallam Ibrahim Ibrahim Gandun Albasa, ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da wakilinmu na Ƴan Zazu, Hassan Mamuda Ya'u, a yau Litinin, lokacin da yake bayyana kaɗan daga irin ƙalubalen da suke fuskanta a sana'ar tasu.
Dattijon ya ce duk da shekaru suna cin musu, amma a haka a kan Kurar turawa suke kwasar Turoso suna zuwa su zubar, a don haka suke kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya shigo cikin lamuran su.
"A cewar sa, "Na shafe sama da shekaru 25, ina sana'ar kwasar Turoso, da ita na aurar da ƴaƴana mata uku, yanzu haka ina da ƴaƴa goma a gida, da mata ɗaya, kuma duk da ita nake ciyar da mu cikin rafin asiri, in ji shi.”
Mallam Ibrahim ya kuma buƙaci matasa da su tashi tsaye wajen riƙo da ƙananan sana'o'i, tare da yin watsi da harkokin daba, da ƙwacen waya, da ma shaye-shayen kayan maye kasancewar ba hanya ce mai ɗorewa ba.
A ƙarshe ya kuma ce za su ƙara bin hanyoyin da suka dace domin ganin an zamanantar da sana'ar da suke yi ta ɗibar Turoso, domin cigaban su da ma sauran al'umma baki ɗaya.



