Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana dalilan hana taron 'Tinubu Must Go' a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa, rashin tabbas game da yanayin tsaro ne ya sanya ta hana gudanar da taron da ƙungiyar da ke adawa da gwamnatin Shugaban kasa Tinubu wato TMG ta shirya a jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema Labarai a ranar Lahadi 11 ga Octoba, 2026.
CP Bakori ya kuma bayyana cewa, ƙungiyar ba ta sanar da rundunar ’yan sanda game da shirya taron ba.
Ya ƙara da cewa matakin dakatar da taron ya zama wajibi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A Lahadin nan ne dai tawagar ƙungiyar ta 'Tinubu Must Go' ta shirya gudanar da taro ƙarkashin jagorancin Barista Abba Hikima Fagge, sai dai taron ya haɗu da cikas inda jami'an tsaro suka hana yi a Kano.



