Koma Labarai
Labarai

Aiki cikin haɗin kai tsakanin lauyoyin gwamnati, yansanda, ma'aikatan Shari'a zai samar da adalci ga al'umma - Kwamishina

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Aiki cikin haɗin kai tsakanin lauyoyin gwamnati, yansanda, ma'aikatan Shari'a zai samar da adalci ga al'umma - Kwamishina

Kwamishinan ma'aikatar Shari'a na jihar Kano Barrister Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ya bayyana cewar aiki cikin haɗin kai tsakanin lauyoyin gwamnati da ƴansanda, da ma'aikatan Shari'a zai samar da adalci ga al'umma.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki a harkokin Shari'a, wanda aka gudanar a jihar kano.

Barrister Maude SAN, ya bayyana cewar gudanar da shari'ar laifuka ta hanyar ƙwarewa zai tabbatar da adalci ga sassan Shari'a.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, taken taron shi ne ingantacciyar hanyar gudanar da shari'ar laifuka cikin adalci da rawar da masu gabatar da ƙara, da yansanda da ma'aikatan Shari'a ke takawa yayin gudanar da shari'ar laifi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM