Koma Labarai
Siyasa

Masu ruwa da tsaki a APCn Kano sun amince da takarar Abba da Tinubu karo na biyu a zaɓen 2027

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masu ruwa da tsaki a APCn Kano sun amince da takarar Abba da Tinubu karo na biyu a zaɓen 2027

Gwamnan jihar Kano kuma Jagoran jam’iyyar Apc na jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kano.

A yayin gudanar da babban taron a jiya Alhamis a gidan gwamnatin Kano, masu ruwa da tsaki a APC sun amince da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, da Gwamna Abba Kabir Yusuf su ci gaba da wa’adi na biyu a kan karagar mulkin su.

A yayin taron dai tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa wa Gwamnan takardun neman takarar Gwamnan karo na biyu a jam’iyyar APC.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƴan siyasa ke ci gaba da nuna sha'awar su ta tsayawa takara a matakai daban-daban.

Ready to PlayDala FM88.5 FM