Gwamnatin Kano ki mayar da hankali wajen inganta walwalar al'ummar jihar - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Awareness for Human Rights and Charity Foundation ta ƙasa, ta ce akwai buƙatar gwamnatin Kano ta dawo da hankalinta a kan al'ummar jihar wajen magance musu matsalolin rashin ruwan sha, da tsaro, da wutar lantarki da kuma ƙuncin talauci da suke ciki, domin inganta walwalar su.
Babban Daraktan ƙungiyar a ƙasar nan, Kwamared Auwal Usman Awareness, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM, a ranar Juma'a 26 ga Yuni, 2026.
Ya ce akwai abin takaici kan yadda gwamnatin Kano, ke nuna halin ko in kula a kan inganta walwalar al'umma a jihar, duk kuwa da irin halin da al'ummar jihar suka samu kan su yanzu a ciki.
Da yake jawabi a kan matsalar tsaro kuwa, Kwamared Auwal Awareness, ya ce akwai tashin hankali kan yadda ɓata gari suke neman hana mutane kwanciyar hankali, domin ko a daren jiya suma sai da wasu ɓata garin matasa suka tare su a yankin Ɗorayi riƙe da muggan makamai.
"A yau jama'a da dama na cikin mawuyacin halin sakamakon rashin ingantaccen tsarin lafiya, da rashin tallafawa matasa da mata da sana'o'in dogaro da kai, don haka akwai buƙatar gwamnati ta fi mayar da hankali wajen gina rayuwar jama'a, mai-makon karkatar da hankalin ta zuwa harkokin kwangila da amfani da tsageru, in ji Auwal Usman.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da dukkanin hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan da suka dace domin ganin an kawo ƙarshen faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye a sassan jihar Kano, domin ƙara wanzar da zaman lafiya a cikin al'umma.



