Koma Labarai
Shari'a

An sake gurfanar da mutanen da ake zargi da kashe ɗan Bijilante, da harbin mata biyu, da kuma garkuwa da Alhaji Kabiru a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An sake gurfanar da mutanen da ake zargi da kashe ɗan Bijilante, da harbin mata biyu, da kuma garkuwa da Alhaji Kabiru a Kano

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 13 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Zuwaira Yusuf, ta sanya ranar 30 ga Yuli, 2026, domin bayyana matsayar ta a kan zargin da ake yi wa wasu mutane.

Gwamnatin jihar Kano, ce dai ta ke ƙarar mutanen da zargin haɗa baki da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma laifin kisan kai.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar a ranar 16 ga Oktoba, 2021, da misalin ƙarfe uku na dare, an yi zargin mutanen da zuwa garin Ɗan sarai da ke ƙaramar hukumar Gezawa, inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Kabiru Shu'aibu.

Kazalika, an kuma zargi cewar mutanen sun harbi mahaifiyar mutumin da matar sa, shi kuma suka yi garkuwa da shi har sai da aka basu Naira miliyan 60 sannan suka sake shi.

An kuma zargi cewar sun kashe wani ɗan bijilante.

A zaman kotun na ranar Laraba 8 ga Yuli, 2026, lauyan gwamnati Lamido Abba Soron ɗinki, ya zo da shaidu uku sai dai lauyoyin kariya sun ce basu shirya ba, inda suka roƙo kotun da ta bayar da beli, sai dai Lamido Soron ɗinki ya yi suka, an kuma ɗage zaman don bayyana matsayar kotun.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, mutanen da ake zargin sun haɗar da Ado Isa gidan ƙara, da Umar Abdullahi ka faɗa kwata, da kuma Shafi'u Adamu, sao kuma Jamilu Akilu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM