Matsalar Tsaro: Masarautar Kano ta janye dukkan hawan Babbar sallar bana a jihar

Majalisar masarautar Kano ta sanar da janye dukkan shirye-shiryen gudanar da haye hayen bikin babbar sallah a jihar.
Masarautar Kano ta bayyana hakan ne ta bakin babban ɗan majalissar Sarki, kuma Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim, a ranar Alhamis 28 ga Mayu, 2026.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne biyo bayan samun shawarwari daga jami’an tsaro, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar yayin bukukuwan Babbar Sallah.
Matakin na zuwa ne bayan da rundunar Ƴansandan Jihar Kano, ta sanar da dakatar da duk wasu harkokin Durbar, da hawan Sallah saboda dalilan tsaro.
A baya dai an sa ran Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da hawan Daushe tare da hakimai, da sauran mahaya a yau Alhamis kafin sanar da janye hawan.
Wakilinmu na Masarautar Kano Manshawi Shu'aibu Uba ya ruwaito cewa, Alhaji Aliyu Ibrahim matawalle, ya kuma buƙaci ɗaukacin al'umma da su yi haƙuri tare da gudanar da addu'o'i na musamman domim samun ɗorewar zaman lafiya a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.



