A shirye nake na yi sulhu da gwamnan Kano Abba Kabir - Sanata Kwankwaso
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar siyasar Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa har yanzu ƙofar sulhu a buɗe take tsakaninsa da Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf duk da saɓanin siyasar da ya faru.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwankwaso ya ce a shirye yake ya yafe wa gwamnan tare da sasanta duk wata rashin jituwa da ke tsakaninsu.
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya kuma jaddada cewa soyayya da ƙaunar da yake yi wa tsohon mabiyinsa ba su ragu ba.
Sai dai wannan na zuwa ne watanni kaɗan da aka jiyo gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, yana gargaɗin cewa ka da tsohon gwamnan na Kano, Rabi'u Kwankwaso ya kai shi bango.


