A gaba na mace ta haihu a kan hanya saboda lalacewar titin yankin mu - Magidanci a Kano

Al'ummar unguwar Tudun Fulani da ke ƙaramar hukumar Ungogo, a Kano, sun koka a kan rashin ingantacciyar hanya da suke fama da ita a yankin su.
Wani magidanci a yankin mai suna Yaushe'u Umar ya bayyana wa Dala FM Kano cewa, Titin nasu ya haɗe da garuruwa guda biyar kuma yana ɗauke da ɗumbin al'umma.
Yaushe'u ya bayyana cewar a gaban sa wata mata ta haihu sakamakon ƙalubalen rashin abin hawa wanda rashin hanyar ya haifar mata a lokacin.
Ya kuma bayyana cewar indai aka yi ruwan sama yaran su basa iya zuwa makaranta saboda rashin kyan hanya.
Yusha'u a madadin al'ummar yankin, sun kuma roƙi gwamnatin jahar Kano da ta kai musu ɗauki domin aikin ya fi ƙarfinsu.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar, mazauna unguwar Tudun Fulani sun kuma ce akwai matsaloli tsubi-tsubi masu kwarfe ruwa a kan hanya domin samun kyakkyawan yanayi na kaiwa da kawowar al'umma a yankin.



