Koma Labarai
Tsaro

Ayi ƙwaƙƙwaran bincike tare da hukunta waɗanda suka kashe malamar islamiyya a Jos - Sheikh Ali Ɗanabba

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ayi ƙwaƙƙwaran bincike tare da hukunta waɗanda suka kashe malamar islamiyya a Jos - Sheikh Ali Ɗanabba

Fitaccen malamin addinin Musulunci, kuma Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya buƙaci ayi bincike tare da hukunta waɗanda suka ɗauki doka a hannu wajen kashe malamar makarantar Islamiyya a mararrabar Jos, da ke jihar Kaduna.

Sheikh Ali Ɗan Abba, ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Facebook, a ranar Litinin 22 ga Yuni, 2026.

A ranar Lahadi 21 ga Yuni, 2026, ne dai wasu musatattun mutane suka kashe malamar makarantar islamiyyar bisa zargin ta da satar yara, al'amarin da ƴan uwan ta, da ma mijin ta suka musanta.

A cewar Ɗanabba, "Ƙyale abin zai ƙara buɗe ƙofar kisan tamore a kan wanda bai ji ba, kuma bai gani ba.”

Malamin ya kuma yi roƙon Allah ya karɓi shahadar marigayiyar, ya kula mata da ƴaƴanta, ya baiwa Mijnta da Iyayenta haƙurin rashin ta.

Hukumomi dai sun daɗe suna buƙatar al'umma da su daina ɗaukar doka a hannu, suna mai cewar idan suka ga wani abu ya faru su rinƙa miƙa shiga zuwa ga jami'an tsaro domin ɗaukar mataki na gaba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM